12 Disamba 2019 - 07:55
Wata Tawagar Tattalin Arziki Daga kasar Rasha Tana Ziyarar Aiki A Iran

Da safiyar yau Laraba ne tawagar tattalin arzikin ta kasar Rasha daga yankin Samara ta iso gundumar Mazandaran da ke arewacin Iran, domin tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

(ABNA24.com) Da safiyar yau Laraba ne tawagar tattalin arzikin ta kasar Rasha daga yankin Samara ta iso gundumar Mazandaran da ke arewacin Iran, domin tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta shaidawa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; tawagar ta kasar Rasha ta zo Iran ne domin fadada alakar tattalin arziki a tsakanin bangarori.

Isafil Amiri ya kuma ce tagawar ta Rasha za ta kai ziyara zuwa yankuna daban-daban na gundumar Mazandaran da ake da kamfanoni da sauran masana’antu, sannan kuma da haduwa da ‘yan kasuwa.

Iran tana da kyakkyawar alaka da kasar Rasha ta fuskoki da dama da su ka hada tattalin arziki da kasuwanci.



/129